Yayinda suke gangami matasan na cewa akwai kwararrun matasa injiniyoyi da makamantansu a Nigeria amma an hanasu damar ba da tasu gudummawa wajen ci da kasar gaba.
Matasan na cewa ayyukan da suka dace a yi cikin gida sai a kai su can Koriya ta Kudu inda matasansu injiniyoyi ke anfana.
Daya daga cikin masu jagorar gangamin zuwa hukumar yaki da cin hanci da rashawa, EFCC, Moses Siyasiya, yace hanasu ayyukan da za su iya yi, ya sa su zama ‘yan kallo a kasarsu.
Wata kungiyar matasa mai suna Connected Development ita ce ta shirya gangamin. Hamza A. Lawal ne kuma shugaban kungiyar tare da hadin kan kungiyar matasa kwararru a fannonin ilimi.
Kungiyoyin biyu sun mika wasikar korafinsu ga hukumar EFCC inda suka bukaci a gudanar da bincike akan lamarin saboda matasa su samu damar baza kolin irin basirar da Allah ya basu. Matasan na ganin abun dake faruwa tamkar cin hanci ne da rashawa.
Bilkisu Ahmed jami’ar yada labarum kungiyar gwagwarmayar ta ce bai kamata a ce ‘yan kwangilar kasashen waje su zo Nigeria su dauki kwangila su kai wasu kasashen ba. Amma ga matasan Nigeria basu da aikin yi. Ta ce ‘yan jarida su taimaka su yada abun dake faruwa domin a jawo hankalin gwamnatin kasa ta yi abun da ya dace. Ta yi misali da kamfanin man Nigeria.
A saurari rahoton Hauwa Umar Udubo domin karin bayani
Facebook Forum