Rahotanni na cewa wasu mahara ne daga kauyukan jihar Filato suka ketaro tare da farma wasu kauyukan kananan hukumomin Karim Lamido da Ibbi na jihar Taraba inda har aka samu asarar rayuka, baya ga dukiyar da suka sace, haka kuma sun yi awon gaba da wasu mutane.
Mr. Naanmi Daniang, Dagacin Fumang, a karamar hukumar Karim Lamido da yanzu haka yake gudun hijira a Jalingo fadar jihar Taraba, ya bayyana yadda aka kai musu hari a Kanshar dawasu kauyuka na yankin.
Shima da yake Karin haske, Hon.Baba Muhammad Usman, kansila dake wakiltar mazabar Ammar, ya ce bai ga wadanda aka kashe ba har ila yau amma maharan sun sace wasu al’umman yankin sun yi awon gaba da su.
Shima wani ganau ya bayyana cewa ba wannan ne karon farko da maharan kan ketaro daga yankin jihar Filato zuwa Taraba don kai hari ba, duk kuwa da matakan da aka dauka a baya.
To sai dai kuma,da Muryar Amurka ta tuntubi daya daga cikin shugabanin al’umman Tarok dake makwabtaka da wadannan yankuna da aka kaiwa harin ya musanta zargin cewa suke kai harin sari-ka-noken.
Tuni aka tura karin jami’an tsaro zuwa yankin don kare rayuka. ASP David Misal shi ne kakakin rundunan ‘yan sandan jihar Taraban ya ce an dau mataki a yanzu.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani
Facebook Forum