Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Da Ake Zargin 'Yan Boko Haram Ne Sun Kai Hari Adamawa


 Dakarun Najeriya Masu Yaki Da ‘Yan Kungiyar Boko Haram
Dakarun Najeriya Masu Yaki Da ‘Yan Kungiyar Boko Haram

Harin dai ya yi sanadiyar kashe dan sa kai guda daya tare da jikkata wasu biyu, sannan suka yi awon gaba da manyan bindigogi biyu na soja.

Akallah an kwashe shekaru uku zuwa hudu kenan ba a samu hare-haren ‘yan Boko Haram ba a jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya, saboda irin matakan tsaro da hukumomin jihar suka dauka.

Wasu da ake zargin ‘yan kungiyar Boko Haram ne sun kai hari kan sojojin da suke zaune a sabon garin Himbla da ke karamar hukumar Madagali.

Harin dai ya yi sanadiyar kashe dan sa kai guda daya tare da jikkata wasu biyu, sannan suka yi awon gaba da manyan bindigogi biyu na soja.

Wani mazauni sabon garin Himbla da ya nemi a sakaya sunansa bisa dalilan tsaro ya ce “’yan bindigar sun kashe wani yaro makocinsa tare da jikkata wasu mutum biyu.” Kuma jami’an tsaron sun yi kokari sosai wajen hana ‘yan Boko Haram din shiga cikin garin.

Shugaban karamar hukumar Madagali Hon. Musa Sashi ya tabbatar da faruwar harin, inda ya ce wasu tsirarun ‘yan Boko Haram sun shigo wani kauye da ake kira Himbla kuma akwai shinge tsaro na sojoji a garin.

Ya ce suna zaton sun zo ne da niyyar su kwashi kayan fada na sojojin kuma garin haka dan bijilante daya ya rasa ransa, sannan ‘yan Boko Haram din sun kwashe bindigogi biyu na sojojin.

Sai dai al'amura sun koma daidai yayin da al’ummar garin suka koma harkokin su na yau da kullum.

Saurari cikakken rahoton Lado Salisu Garba:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:01 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG