Bayan wasan tamola, wasan kwallo mai raga ‘Basket ball’ na kara zama wasa da ke shiga cikin ra’ayin matasa a fadin duniya. Wasan kwallon raga a kasar Amurka na kara shiga cikin jerin wasannin da su kayi fice.
Kungiyar kwallon raga ta kasa-da-kasa a Amurka nada ‘yan wasa 113, wanda kashi daya 1% cikin uku 3% na matasan sun fito daga wasu kasashe a fadin duniya ne. Kasashen sun hada da kasar Poland, kasar Czech Republic, sai wasu kasashen Afrika.
A cewar daya daga cikin ‘yan wasan Ian Mahinmi, wanda mahaifiyar shi ‘yar kasar Jamaica, kana mahaifin shi kuwa dan asalin kasar Benin ne, a yankin Afrika maso yamma. Matashin mai shekaru 28, yace wasan kwallon mai raga wasa ne da yake da muhimanci ga lafiyar matasa.
Kuma wasa ne da zai ba matasa damar iya dogaro da kai, domin kuwa mutun zai samu kudi matuka, idan har yana da hazaka wajen maida hankali, domin wasa ne da kawai yake bukatar sanin makama da duk dubaru.
Hakan yasa yanzu haka ya daukar ma kanshi cewar, duk shekara zai dinga ware wasu watanni don zuwa kasashen Afrika, don koyar da dubarun wasan kwallon mai raga ga matasa. Yana ganin cewar akwai matasa da suke da basira ‘yan kasashen Afrika, da ake da bukatar su a fagen wannan wasan.
Domin wasa ne da yake bukatar matasa masu tsawo, lafiyar jiki, da kuma sha’awa. Haka shima kocin wata kungiya mai suna Washington Wizards, ya bayyanar da irin bukatar da ake da ita na samun ‘yan wasa da suka fito daga kasashen Afrika.
Domin ya zuwa yanzu yaga matasa daga wasu kasashe da suke taka muhimmiyar rawa, a fanin wasan kwallon raga. Don haka yana kara bama matasa kwarin gwiwa, da su tashi tsaye wajen shiga wasan baske ball kamar yadda suke sa kansu cikin wasan tamola.
Facebook Forum