A Najeriya, ana yawan tsangwamar zabaya sosai ana kuma kyamatarsu ko ma a kashe su. Wani zabaya yana kokarin canza yadda abubuwa suke tafiya a masana’antar fina finan Najeriya. Kwarjinin da yake samu yanzu na karfafa gwiwar sauran zabayoyin da yawa.
Damilola Agunsi dan shekaru 40 da haihuwa, wanda aka fi sani da lakabin sunan Gold Fish, zabaya ne dake da babban guri.
A lokacin da yake matashi, Ogunsi ya fuskanci wariya sosai amma ya ce yin wasa a fina finai ya bashi dama shi ma a ji shi.
Kafin ya fara wasan fina finai, Ogunsi yayi aikin banki kusan shekaru 10.
A yanzu, yana yawan fitowa a fina finan Najeriya sosai, ko da yake akwai babban gurin da yake so ya cimma a rayuwarsa.
Ogunsi ya ce, shi a ganinsa zai iya fitowa a matsayin James Bond, ko Batman ko kuma Iron Man ne. irin fitowar da yake so yayi kenan a fina finai. Kuma ya ce yana horar da kansa akan cimma wannan gurin.
Akwai zabayoyi kusan miliyan 2 a Najeriya, a cewar wata gidauniyar zabayoyi dake birnin Abuja. Da yawansu suna fuskantar tsangwama da wariya kusan duk rana.
Facebook Forum