A Janhuriyar Nijer mako biyu bayan da jam’iyyar CDS Rahama ta gudanar da taronta na kasa, wasu shugabannin jam’iyyar Sun bayyana shirin shigar da kara a gaban kotu saboda a cewarsu ba da yawunsu aka shirya wannan taron da a karshensa aka zabi Bubakar Madugu a matsayin sabon shugaba ba.
Rashin yarda da halaccin wadanda suka wakilci rassan jam’iyyar ta CDS Rahama a wurin wannan taro da ya bayyana Me Madougou Boubakar a matsayin sabon zababben shugaban jam’iyyar na kasa baki daya ya sa bangaren tsohon shugaba Abdou Labo soma shirye shiryen maka abokan hamayyarsu a kotu akan bukatar ta soke dukkan shawarwarin da taron na Yamai ya tsayar.
Malan Abdou Ammani na kan gaban wannan yunkurin. Yace su ba su ki a sasanta ba amma wancan bangaren sun ga shirin ba zai gyara su ba. Bayan haka akwai ka’idodin zama shugaba a jam’iyyar.
Kamar yadda bangaren Labo ke kallon bangaren Madougou da rashin cancantar tafiyarda harakokin jam’iyya, haka dayan bangaren ke cewa tun jimawa doka ta yanke hukunci akan makomar siyasar Abdou Labo inji Malan Moutari Kadri, kusa a bangaren Me Madougou Bouabkar.
Facebook Forum