Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Jirgi Ya Yi Hadari A Ibadan


Tsoffafin Hotuna:
Tsoffafin Hotuna:

Wani jirgin mai lamba N580KR , dauke ne da wasu muhimman mutane da kawo yanzu ba a bayyana sunayesu ba, ya yi hadari a Ibadan, babban birnin jihar Oyo a kudu maso yammacin Najeriya.

Jirgin ya kau wa hanyarsane a lokacin da yake kokarin sauka a Ibadan da ga birnin abuja.

Rahotannin dake fitowa daga kusa da filin jirgin saman na Ibadan sun nuna cewa mutane goma ne suke cikin jirgin kuma babu wanda ya mutu ko yayi rauni.

Tuni dai jamian kashe gobara suka garzaya wajen hadarin don hana tashin wuta da kulawa da fasinjojin.

Kakakin Hukumar Kula da Jiragen Saman Najeriya Carol Adekotujo wadda ya tabbatar da hadarin yace sun tura jamiansu wajen don binciken dalilin hadarin

Ga cikkaken rahoton Hassan Umaru Tambuwal daga Ibadan, Babban birnin jihar Oyo.

Wani Jirgin Sama Ya Yi Hadari A Ibadan
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:47 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG