Hukumar 'yansandan fararen kaya ko SSS ta fito fili ta bayyana cafke Air Commodor Muhammad Umar, daya daga cikin mutane goma sha uku da shugaban Najeriya ya nada domin su binciki badakalar sayen makamai biyo bayan kamun da aka yiwa Kanal Sambo Dasuki mai ba tsohon shugaban kasa shawara akan harkokin tsaro.
Hukumar tana zargin Air Commodor Muhammad Umar da cin hanci da rashawa da kuma tsayawa wasu kusoshi a gwamnatin Buhari, musamman na bangaren tsaro da na bincike na jagorancin karbar cin naci da rashawa.
Ita hukumar EFCC tuni ta fito tayi tur da zargin cewa akwai jami'anta akan zarge zargen da ake yiwa Air Commodor Muhammad Umar mai ritaya. Hukumar ta fito ta musanta batun ne domin kokarin da wasu su keyi na danganta hukumar da ofishin mai ba shugaban kasa shawara akan harkokin tsaro.
Hukumar ta EFCC ta yi kira a gudanar da cikakken bincike domin a bi digdigin maganar a san gaskiya domin kada ayi anfani da lamarin a karkatar da akalar binciken badakalar sayen makamai.
Akan haka ne shugaban kungiyar kishin 'yan arewa Dr. Junaidu Muhammad ya yi gargadin cewa lokaci ya yi da za'a yi takatsantsan akan irin abubuwan dake faruwa a cikin gwamnatin Muhammad Buhari dangane da yaki da cin hanci da rashawa.
Yace Air Commodor Umar kadai ake bincike cikin mutane goma sha uku cewa ya karbi cin hancin nera miliyan daya da rabi amma tun kafin wannan lamarin, binciken kansa ya cutura. Dalilin kuwa shi ne saboda wasu manya manya a cikin gwamnatin Buhari da wasu 'yanuwansa na jini suna da alaka da wasu da ake bincike musamman a cikin manya manyan sojoji da aka yi masu ritaya.
Yace mutum daya bai isa ya hana ko ya dakatar da bincike ba cikin mutane goma sha uku da aka basu aikin tare. Idan akwai badakala dole akwai wadanda suka yi tare. Dr Junaidu yace sun san akwai wasu takardu da suka shafi shekara 2007 zuwa 2011 da aka gagara dubasu saboda wasu masu karfi, musamman wani babban hafsan hafsoshin soja da binciken ka iya shafa. Yana ciki ya yi kane-kane kuma yana da alaka da shugaba Buhari.
Idan ana son a yi gaskiya to a duba duk wanda yake cikin kwamitin binciken a kuma bayyana a fili laifin shi Commodor Umar.
Ga karin bayani.