Dakta Kabir Abdulkadir ‘Yammama wani masani ne na irin arzikin kasar da jihohin Najeriya suke da su binne a kasa da kuma wadansu da ake samu ta hanyar noma wanda ko da wadannan aka dogara jihohin za su rike kansu har ma su taimaki wasu makwabtansu.
A misa idan ka nufi garuruwan kabilar Igbo an san su da arzikin kwakwa kuma suna kan gaba a yin man kwakwa. Misali in ka nufi wuraren Fatakwal, Abia, Enugu da Imo duk suna da arzikin kwakwa.
Kudu maso yamma a Najeriya kuma suna da arzikin itacen koko a jihohi kamar su Ondo, Osun da Oyo. Arewacin Najeriya ta tsakiya kuma irin su Benue suna da kayan marmari irin su Lemo, Mangwaro, Ayaba da sauransu.
Arewa maso gabas Borno itace kan gaba wajen itacen Karo. Kano da Gombe suna noman tumatur sosai. Idan aka je annkin hawan Mambila ta jihar Taraba kuma yana da yanayin kasashen Turai wanda ko kudan tsando bay a iya rayuwa balle ya cutar da mutane da dabbobin wajen.
Haka kuma a Mambila din za a iya shuka ko wace irin itace ko shukar da sai a Turai ta ke fitowa. Idan muka koma kan fatar Shanu a Najeriya, fatar kasar ta fi na ko ina inganci. A jihar Katsina da Jos a bangaren jihar Filato kuma nan ake samun auduga. Kano nan aka fi yin noman gyada.
Arewa na da man fetur a karkashin kasa saboda muna da kwal. Mun ma fi Kudancin Najeriya yawan kwal. Tun daga Benue, Abuja, Kaduna, Jos har zuwa Gombe, Bauchi da Taraba.
Daga karshe Dakta ‘Yammama ya yi kira da a kalli mutumin da ke da hangen nesa wanda zai iya alkinta dukiyar da Allah ya albarkaci jiha da ita wajen amfanar da al’ummarsa.