Kade-kaden Afirka na bazuwa ko’ina a fadin duniya saboda yadda ‘yan nahiyar ke karuwa a sassan duniya daban daban, kuma ba wai kawai ‘yan Afirka mazauna kasashen waje ne ke taka rawa ga irin kade-kaden ba.
Wakokin zamani da ake kira Pop da turanci daga nahiyar Afirka na bazuwa zuwa ko ina a duniya, kama daga can Afrika har zuwa nan birnin Washington DC.
Wakokin da aka fi sani da Afro-pop ko Afrobeats, a da, ‘yan Afirka kadai ke saurarensu, amma yanzu sun sami karbuwa har a kasashen yammacin duniya.
“Abin jin dadi ne matuka ganin mawakan da mafi yawanmu muka sansu a Afirka, yanzu ana jin su a gidajen radiyon manyan biranen duniya kamar birnin New York ko DC, ko kuma gidajen rediyo irin na birnin Iowa. Kuma mutane sun fara maida hankali garesu,” a cewar Mercy Chikowore.
Wakokin Afrobeats sun sami karbuwa a ‘yan shekarun nan, musamman wadanda aka hada su ta hanyar cudanya a tsakanin fitattun mawakan Amurka irinsu Chris Brown, da Drake da kuma Rick Ross.
“Wadannan mawakan a koda yaushe suna da masu bibiyarsu. Ko da ace kai Burna boy ne, ko Yemi Alade ko wasu kamar su, kuma kana Najeriya, akwai ‘yan Najeriya dake zaune a duk fadin duniya. Saboda haka a koda yaushe duk inda ‘yan Najeriya suka je wakokin da kade-kade zasu bi su.
Facebook Forum