Kwamatin sulhun MDD yayi kira ga hukmomin kasar Libya das u dauki matakan hana bazuwar Makamai masu linzami zuwa yankunan dake Makwabtaka da Libya. Kwamatin sulhun yayi wnanan kiran ne a dai dai lokacin da hukumomin wucin gadi kasar suka zabo sabon friministan wucin gadi wanda zai yi jagorancin shirin sauyin siyasr da ake yi a kasar Libya.
Gefe guda kuma, Majalisar Mulkin Wucin gadi ta kasar Libya ta zabi Abdel Rahim el-Keeb a matsayin sabon friministan wucin gadi. Litinin da ta gabata ce ‘yan majalisar mulkin wucin gadin suka suka zabi El-Keeb da kuri’u 26 daga cikin 51. El-Keeb injiniyan lantarki ne wanda yayi karatu a a Amurka, kuma shine zai yi jagorancin kafa sabuwar Gwamnati a Libya har zuwa lokacin gudanar da sabon zabe.