Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wakilan arewaci da kudancin Sudan zasu gana akan batun yankin Abyei


Motar a kori kura, mallakin rundunar mayakan Sudan, take wucewa kusa da gine ginen da suke konewa a tsakiyar Abyei.
Motar a kori kura, mallakin rundunar mayakan Sudan, take wucewa kusa da gine ginen da suke konewa a tsakiyar Abyei.

An shirya a yau asabar wakilai daga yankin arewaci da kudancin Sudan zasu gana a hedikwatar kungiyar kasashen Afrika domin tattauna batun yankin Abyei da sojojin arewacin kasar suka mamaye, al’amarin daya tado rikicin jin kai.

An shirya a yau asabar wakilai daga yankin arewaci da kudancin Sudan zasu gana a hedikwatar kungiyar kasashen Afrika domin tattauna batun yankin Abyei da sojojin arewacin kasar suka mamaye, al’amarin daya tado rikicin jin kai. Wannan tattaunawa da za’a yi a birnin Addis Ababa kasar Ethiopia, za’a yi ne kwana daya bayan da wani jami’in kudancin Sudan yace mutane dubu tamanin ne suka arce daga Abyei.

Majalisar Dinkin Duniya tace dubban mutane suna zaune a filin Allah ta’ala, ba tare da isashen kayayyakin abinci ko mai ba. Yanzu haka wakilin Amirka a Sudan Princeton Lyman yana kan hanyarsa ta zuwa Qatar daga can ya wuce kasar Sudan domin tattauna al’amarin na Abyei. Ana sa ran zai bukaci jami’an Sudan da suyi wa Allah su magance sauran batutuwa tsakanin yankin arewaci da kudanci da ba’a magance su ba, kafin yanki kudanci ya ayyana samun yanci a ranar sha tara ga watan yuli idan Allah ya kaimu.

Bangarorin biyu suna da sabanin akan makomar yankin Abyei. Shugaba Omar Al Bashir yace wannan yanki zai ci gaba da kasancewa karkashin ikon yankin arewaci.

XS
SM
MD
LG