Biyo bayan dawowar wakilan taron kasa wailiyar Muryar Amurka ta zanta da daya daga cikinsu, Ambassador Ibrahim Mai Sule kuma daya daga cikin 'ya'yan kungiyar dattawan arewa.
Idan dai ba'a manta ba tun kafin a fara taron wasu 'yan arewa suke korafin cewa taron bashi da alfanu ga arewa. Sabili da haka wakiliyar Muryar Amurka ta fara da tambayarsa alfanun taron ga arewa. Ambassador Ibrahim yace taron yana da alfanu ga arewa domin an kare wasu abubuwa da basu kamata a yi ba.
Ya kawo misalin batun kirkiro jihohi wanda yace ba wai an amince ba ne sai dai wasu sun kawo sunayen sabbin jihohin kana sai aka yi kamar an yadda. Yace irin wannan maganar dole ta koma majalisa domin su ne zababbun wakilai kuma mutane su gane su tabbatar sun gayawa 'yan majalisunsu abubuwan da suke so.
Ambassador ya bayar da shawara akn yadda za'a aiwatar da wasu abubuwa. Yace a kasasu kashi uku. Na farko a dauki wadanda gwamnati zata iya yi ba tare da yin doka ba domin gwamnati ta bi hanyoyinta na aikatar dasu. Na biyu akwai wadanda suke bukatar yin doka ta kasa domin a yi anfani dasu. Sai a kaiwa majalisa ta yi dokokin da suka dace amma ba wai ayi wani sabon tsarin mulki ba. Na uku a mayar da kananan hukumomi karkashin jihohi kuma a ba jihohi ikon kirkiro wasu kananan hukumomi idan suna bukata.
Cikin abubuwan dake kunshe a rahoton da zasu mika har da batun yadda aka tsara hukumar zabe. Wakilan suna ganin ya kamata a koma akan tsarin da zai kafa hukumar zabe mai zaman kanta a zahiri. Akwai yadda za'a samu hukumar zabe mai zaman kanta da kuma cikakken iko wadda ba gwamnati zata nadata ba.
Ga cikakken rahoton Medina Dauda.