Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wajibi Ne A Dauki Mataki Kan Gwamnatin Assad Domin Amfani Da Makamai Masu Guba


The White House
The White House

A watan nan na Afrilu aka cika shekaru biyu da munanan hare-haren makamai masu guba a Syria: na farko a ranar 4 ga Afrilu, 2017 lokacin da gwamnatin Assad ta tura makamai masu guba a garin Khan Sheikhoun da ke Idlib; na biyu a ranar 7 ga Afrilu, 2018 akan garin Douma.

Hare-haren – gubar na janyo shakewa – abin da ya kashe mata, maza da yara da yawa, kuma ya raunata darurruwa.

Bayan Yaƙin Duniya na farko, lokacin da aka yi mummunar azabtarwa na makamai masu guba a cikin mummunan yanayi, da farko ƙasashen duniya sun fara hana amfani da su, sannan kuma suka haramta samar da su, da ma adana su.

Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar hana amfani da makamai masu guba, wadanda aka fi sani da OPCW sun tabbatar da amfani da makamai masu guba da gwamnatin Assad ke yi.

Da take jawabi a taron Majalisar Dinkin Duniya na kwanan nan game da makamai masu guba a Syria, Wakiliyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Linda Thomas-Greenfield ta sake jaddada goyon bayan Amurka ga "aikin rashin nuna son kai na OPCW da hukumomin binciken ta."

Ambasada Thomas-Greenfield ta lura cewa taron na OPCW mai zuwa na kasashe daban-daban, na ba da dama ga kasashen duniya “su aike da sako mai karfi ga gwamnatin Assad cewa ba za a amince da amfani da makami masu guba ba kuma akwai mummunan sakamako da zai biyo bayan amfani da su.

Ta bukaci kasashen da su dauki tsauraran matakai tare da kada kuri’ar amincewa da wani daftarin matakindakile dama da Syria ke da ita, karkashin Yarjejeniyar Makamai Masu Guba.

Da yake tuno da shaidar a gaban Kwamitin Tsaro na Dokta Amani Ballour, wanda ya yi aiki na tsawon shekaru a Syria, Ambasada Thomas-Greenfield ta lura cewa mafi munin daren rayuwar likitan “shi ne lokacin da ta isa wani asibiti inda yara su ke kasa lumfashi bayan sun shaki guban . ”

"Mata da yara na Syria na jira," in ji Ambasada Thomas-Greenfield. “Sun san cewa Kwamitin Tsaron ya ce ba za a amince da kai harin makamai masu guba ba. Sun san muna da karfin da za mu dauki matakan kangwamnatin Assad. Don haka, bari muyi aiki. Kuma bari mu nuna musu cewa mun cancanci ikon. ”

XS
SM
MD
LG