Ganin cewar yanzu kasa da kwanaki 50 suka rage a yi zabe a Najeriya, amma masana nagani cewar jam’iyar PDP ta kwashe shekaru sama da goma shashida (16) suna mulki, kuma suna tunkaho da yawan gwamnoni da suke da su a kasar da ‘yan majalisar dokoki a matakan tarayya da jihohi. Ba ta tsinana ma talaka komai ba a kasar, tabakin wani masanin kimiyar siyasa a kasar, Mal. Abbati Bako, yace jam’iyar tayi suna a duniya, sai dai tasamu matsala wanda ta haddasa rashin tsaro a wannan lokacin, cin hanci da rashawa, harma da matsaloli da suka shafi dangantaka da kasashen duniya ma. A zahirin gaskiya yanzu mutuncin da darajar Najeriya yana kara ragewa ne a idon duniya, duk wanna ya faru ne a sanadiyyar mulkin PDP. Yace a mahanga na ilimi, jam’iyyar nada jan aiki a gabanta kamin tasamu ta gamsar da mutanen Najeriya.
Ita kuma jam’iyar APC na tunkaho ne da dan-takarar ta wanda talakawan Najeriya ke sonshi, a wani hannu kuma attajiran kasar na shakkar makomarsu idan dan-takarar jam’iyar APC yayi nasara. Tabakin Bashir Hayatu Jetli, Idan dai har Janar Muhammadu Buhari zai yi yadda tsohon shugaban kasar Afrika ta kudu yayi, bayan fitowar shi daga gidan kasu Nelson Mandel, dayace duk wanda ya saci dukiyar kasar to anyafe mishi amma za’a fara sabuwar gwamnati wanda duk wanda yayi kuskuren sata a yansu to za’a hukuntashi. Ta bangaren malaman addinai kuwa, batun yima juna afuwa, itace hanyar da za’abi don ciyar da kasar gaba da bunkasar tattalin arzikin, tabakin Mal. Muhammad Dauda, yace ko zamanin annabawa anyi ahuwa ga duk wadanda sukayi wani laifi. Kuma yace, a musulunci idan akwai wani gyara da za’ayi wanda wannan gyaran zai iya haifar da matsalar da ta fi gyaran to mafi kyawo shine a bar wanna gyaran don zaman lafiya.