Wani jami’in Majalisar Dinkin Duniya a Ivory Coast ya ce dakarun da ke biyayya ga shugaban Ivory Coast da ke kan gado Laurent Gbagbo, na ta harbe-harben kai mai uwa da wabi kan wuraren da su ke jin masu goyon bayan Alassane Ouattara ne.
Jami’in rajin kare ‘yancin dan adam Guillaume Ngefa ya fadi a wani taron manema labarai a yau Alhamis cewa wannan harbe-harben da sauran hare-haren sun hallaka a kalla mutane 50 a makon jiya, ciki hard a yara 5 bayan dinbin wadanda su ka sami raunuka.
Ngefa wanda ke magana daga birnin Abidjan, y ace hare-haren sun sa adadin wadanda su ka mutu tun farkon rikicin day a biyo bayan zaben ya kai mutane 462.
Gbagbo dai ya yi biris da kiraye-kirayen Majalisar Dinkin Duniya, da Tarayyar Afirka, da kuma wani bangare na Afirka wato ECOWAS cewa ya mika ragamar iko. Dukkannin wadannan hukumomi ukun sun ayyana Mr. Ouattara a matsayin wanda ya ci zaben shugaban kasar da aka gudanar a watan Nuwamba.