Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wadanda Mu Ke Wa Aiki Na Daukar Mu Tamkar Bayi- 'Yan Matan Malawi A Oman


Wasu mata na gangamin adawa da aikin cin zali
Wasu mata na gangamin adawa da aikin cin zali

Gwamnatin kasar Malawi tace, tana fuskantar kalubale wajen maida kimanin mata su 60 da aka yi safarar su zuwa Oman, da su ka yi korafin cewa, suna aiki a mummunan yanayi mai kama da bauta.

A Shekarar 2022 ne wasu mata suka ankarar da hukumomin kasar Malawi ta hanyar rubuce rubucen da suka rika yi a kafar sadarwar zamani, inda suka bayyana cin zarafin su da wadanda suke wa aiki ke yi, na azabtar da su ta hanyar lalata da rashin mutunta diyaucin su.

Sakamakon haka ne a bana, gwamnatin Malawi tace, ta ware kudi kimanin dala dubu dari uku da hamsin ($350,000) domin aikin maido da 'yanmatan gida, duk da dai an hana tawagar damar shiga Oman domin fara aikin. To amma duk da haka wasu 'yan matan sun samu komowa gida da taimakon kudi daga iyayen su da kungiyoyi masu zaman kansu.

Wadansu matan Indonesia da aka tasa keyarsu daga Malaysia
Wadansu matan Indonesia da aka tasa keyarsu daga Malaysia

Ita dai kasar Malawi bata da wata huldar diplomasiyya da Oman. Gwamnatin ta Malawi ta yanke shawarar aikin maido da 'yan matan gida ne, bayan sakonnin korafin data samu daga 'yan matan da akayi safarr su a watan Fabrairu, amma kokarin aikewa da tawaga zuwa Oman domin fara aikin maido da yammatan gida yaci tura, sakamakon rashin samun takardar izinin shiga kasar.

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Malawi, John Kabaghe, yace, gwamnatin Malawi na duba wasu hanyoyin da za a iya bi domin maido da matan gida, da ya hada da yin aiki tare da wasu kungiyoyi masu zaman kansu dake Oman, da zasu taimaka a kai ga nasara.

Ya zuwa wannan lokacin, kimanin 'yan mata 21 'yan asalin Malawi dake Oman sun dawo gida. Sai dai wani abin takaici shine, jin labarin cewa, a yayin da ake wannan kokari, wasu matan na ci gaba da barin Malawi zuwa Oman, inda suke tsintar kansu cikin irin matsalar da ake magana a kanta.

Da dadewa wasu mayaudara bata gari, ke yaudarar 'yan kasar Malawi da alkawarin samar masu ayyukan yi masu gwabi a kasashe irin su Oman, Qatar, da hadaddiyar daular larabawa, inda da dama kan bige da yin wasu ayyukan na dabam, da basu aka yi musu alkawari ba tun da farko, cikin mummunan yanayi.

Misali, akwai wani labari da aka yi ta yadawa a shafin Facebook, a bara, inda wata mata 'yar Malawi da taje aiki a Oman, ta bayyana irin wulakanci da cin zarafi da ta fuskanta, da suka hada da fyade, azabtarwa da biyan ta albashin da bai taka kara ya karya ba, ta danganta halin data shiga da tsantsagwaron bauta.

Mata na aiki a gona
Mata na aiki a gona

Ko a watan Yunin da ya gabata, sai da wata jarida a Malawi ta buga labarin wata 'yar asalin kasar mai shekaru 23 data rasu a Oman, a wani asibiti mai zaman kan shi, bayan da wanda take ma aiki ya ajiye ta a asibitin ya kama gaban shi. Daga bisani aka zo da gawar ta gida aka binne.

Hakan yasa a watan Fabrairu, wata kungiya mai zaman kanta da cibiyar nazarin tsare tsaren tattalin arziki da demokradiyya a Malawi, suka kaddamar da wani shiri na neman tara kudi dalar Amurka dubu biyu da dari hudu($2,400) domin ceto mata 60 dake cikin halin kakanikayi a Oman.

Shugaban kungiyar, Sylvester Namiwa, yace, hankalin su ya tashi matuka, bayan da suka kalli faifan bidiyon da ya nuna matan suna zayyana irin mawuyacin halin da suke ciki, inda suke rayuwa da gutsuren burodi biyu da kwalbar ruwa daya a rana, baya ga lalatar da ake yi dasu yadda aka ga dama.

Mata da kananan yara na dibar ruwa a Malawi
Mata da kananan yara na dibar ruwa a Malawi

Yace, hakan yasa suka zabura domin ganin anyi wani abu akai, amma yace hakar su bata cimma ruwa ba, musamman, a daidai lokacin ne kasar ta fuskanci iftila’in mahaukaciyar guguwa nan mai hade da ruwa ta Freddy, lamarin da yasa baki daya, hankali ya koma kanta.

Ita ma shugabar hukumar kula da hakkin bil’adama ta Malawi, Emma Kaliya tace, suna da labarin cewa, wasu yan kasar ta Malawi sun bar kasar zuwa wasu kasashe, sakamakon matsalolin tattalin arziki da jama’a da dama ke fama da su. Tace, sai dai duk da haka, ya kamata mutane su rika yin nazari kafin barin kasashen su dayin takatsantsan.

~Hauwa Sheriff~

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG