A wata ziyara da ya kai yankin, Babban editan Muryar Amurka Alhaji Aliyu Mustapha Na Sokoto ya ziyarci jihohin Bauchi da Gombe.
"Na farko na zo ne na sada zumunci a madadin gidan rediyonmu na Muryar Amurka tare da jaddada dangantaka dake tsakanin Muryar Amurka da kafofin yada labarai dake yankin, musamman jihohin Gombe da Bauchi." In ji Mustaphan Sokoto.
Ya kara da cewa ziyarar ta shi ta kuma kunshi yayata wani shiri na musamman da Muryar Amurka ta shirya na bidiyo tare da bayanai akan kungiyar ta'adancin nan ta Boko Haram.
Ya ce suna son mutane su fahimci cewa abubuwan da kungiyar ta ke yi ba Musulunci ba ne.
"Ba inda Musulunci ya ce ka yi kabbara ka shiga masallaci ka hallaka mutane". In ji shi.
Mustaphan Sokoto ya ce idan suka kulla yarjejeniyar cude-ni-in-cudeka za su yi.
Ya ce na farko za su dinga musayar shirye-shirye a tsakaninsu, sannan suna iya samun horaswa daga Muryar Amurka ko a cikin Najeriya ko kuma nan Amurka idan ta kama a yi hakan.
Ya kuma kara da cewa, za su samar da agajin kayan aiki irin na zamani.
Malam Ibrahim Idris Abubakar shugaban gidan talibijan na jihar Bauchi ya ce sun dade suna da yarjejeniya da Muryar Amurka, kuma sun sabuntata ba da dadewa ba.
Ita kuwa Sa'adiya Ibrahim, Janar Manaja ta Progress FM dake Gombe ta ce yanzu suna shirye-shiryen hada alaka ne da Muryar Amurka da suke ganin za ta amfane su baki daya.
Gidado Umaru Kumo shugaban gidan radiyon Ray Power Gombe ya ce sun tattauna da shugabanninsu kuma sun amince za su hada dangantakar da Muryar Amurka domin a samu karin ilimantarwa.
Shi ma Faruk Mu'azu Gombe daga gidan rediyo mallakar jihar Gombe ya ce hada alaka da Muryar Amurka abu ne mai muhimmanci kuma ya yi imani dangantakar za ta taimaka sosai.
Ga rahoton Abduwahab Muhammad da karin bayani.