Dan wasan baya na kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, wanda ya lashe kyautar gwarzon dan wasan kungiyoyin kwallon kafar Ingila a bana Van Dijk, yace har yanzu idan ya tuna abunda Barcelona ta yiwa tsohuwar kungiyar shi ta Celtic ransa ya kan baci.
A wannan lokacin Barcelona dai ta lallasa kungiyar kwallon kafa ta Celtic daci 6 -1 a shekarun baya a gasar cin kofin zakarun Turai, sai dai a lokacin dan wansata Messi bai buga wasa ba.
Dan wasan Van Dijk, yace wannan shine lokacin da zai dauki fansa na rama abin da Barcelona tayi wa tsohowar kungiyarsa ta Celtic, domin tun daga wannan ranar dan wasan yace bai sake buga wasa a Nou Camp fili mai tarihi, amman yana fatan wannan lokacin komai zai canza domin yana cikin tawagar kungiyar da zasu iya samun nasara a kan Barcelona kuma a gidanta.
Barcelona dai zata karbi bakoncin Liverpool ne a yau Laraba 1 ga watan Mayu 2019, cikin gasar cin kofin zakarun Turai na bana a matakin wasan daf da na karshe karawar farko.
Facebook Forum