Asusun tallafawa yara na Majalisar Dinkin Duniya ko UNICEF yace a Najeriya akwai kimanin yara miliyan goma da dubu dari biyar da basa makarantar boko.
Wakiliyar asusun a Najeriya ita ta fada haka yayinda ta kai wa gwamnan Bauchi Alhaji Muhammad Abubakar ziyara.
Wakiliyar tace wannan yanayin bai kamata a bari ya cigaba haka ba domin ba zai haifar wa kasar da mai do ba, wato a bar miliyoyin yara basa zuwa makaranta. Tace zasu yi iya kokari domin rage yawan yaran da basa makaranta.
Tayi alkawari cewa asusun zai duba tsarin karatun islama da zai yi daidai da manhajan karatun boko.
Jihar Bauchi na cikin jihohin da asusun ya dade yana aiwatar da aikinsa. Saboda haka asusun zai cigaba da ayyukansa a fannonin ilimi, kiwon lafiya da tsaftace muhalli da wasu na jin dadin jama'a.
Yayinda yake nashi jawabin gwamnan jihar Bauchi Alhaji Muhammad Abubakar ya tabbatar da ba asusun goyon baya ga duk shirin ayyukansa a jihar. Jihar Bauchi zata shiga cikin ayarin jihohin dake bada tallafi. Gwamnan yace kowane wata gwamnatinsa zata kebe wani kaso saboda tallafawa ayyukan asusun.
Ga rahoton Abdulwahab Muhammad.