Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

UNESCO Ta Ayyana Tufafin Kente Na Ghana A Matsayin Kayan Tarihi


Kente wanda ya samo asali daga al’ummomin Asante da Ewe na kasar Ghana, ya yi fice a duniya saboda dara-daran launukansa.

Hukumar bunkasa tarihi da al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya (UNESCO) ta shigar da sunan fitaccen tufafin Kente na kasar Ghana cikin jerin kayan tarihin dan adam.

Karbar da duniya ta yiwa Kente karkashin yarjejeniyar kasa da kasa ta 2003 akan alkinta kayayyakin tarihi ta kara fito da tasirin tufafin mai launuka da ake sakawa da hannu.

Kente wanda ya samo asali daga al’ummomin Asante da Ewe na kasar Ghana, ya yi fice a duniya saboda dara-daran launukansa.

Ministan yawon bude idanu Andrew Egyapa Mercer ya bayyana karramawar da Kente ya samu a matsayin wata shaida ta jajircewar Ghana wajen alkinta kayan tarihi da al’adu.

“Wannan nasara ta sanya Ghana a sahun gaba a kokarin duniya na alkintawa da mutunta al’adu,” a cewarsa.

Dandalin Mu Tattauna

Bidiyo

Saurari Dalilin Da Ya Sa Ummi Zeezee Ta Ce Tana So Ta Kashe Kanta A Hira Da Wakiliyar VOA Baraka Bashir
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:39 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Saurari Bayanin Jarumar Kannywood, Nafeesa Abdullahi
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:24 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Bikin Yini Na Auren Zawarawa A Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG