Dan wasan tamaula na kungiyar kwallon kafa ta Zaragoza (a kasar Spain), Ikechukwu Uche, ya zub da hawaye yana kuka jiya laraba a bayan da ya jefa kwallonsa na farko tun komowarsa daga mummunan raunin da ya ji a guiwar kafarsa.
Wannan kwallon da Uche dan Najeriya ya jefa ya ba kungiyarsa damar doke kungiyar Athletic Bilbao da ci 2-1.
A bayan da abokan wasansa na kungiyar Zaragoza suka rufu kansa su na taya shi murnar wannan kwallo da ya jefa a minti na 55, Uche ya mike tsaye inda aka ga hawaye na zuba babu tsattsayawa daga idanunsa a bayan da ya jefa kwallon nasa na farko a kulob dinsa tun watan Mayun 2009.
Wannan shi en karon farko da aka fara buga wasa da Uche tun lokacin da aka yi masa tiyata a watan Agusta, kuma shi en karo na uku da yake buga wasa. Wasu jijiyoyi a guiwar Uche ta kafar hagu sun tsinke, abinda ya sa ya kasa buga wasa na kusan dukkan tsawon shekarar da ta shige. Da ma dai ya taba jin rauni a wannan kafa ta sa ta hagu.