Har yanzu ana zaman dar dar a babban birnin Tunisia,yayinda shugaban riko ya kama ragama daga shugaban Aksar da ya fi dadewa kan mulki, da borin jama’a ya tilasta masa barin kasar.
Rahotanni na cewa anji harbe harben bindiga a birninTunis jiya Asabar, yayinda ‘yansanda da motocin sojoji masu sulke suke sintiri akn tituna birnin dake cike da shara, sakamakon zanga zanga da dibar ganima cikin dare.
Kamfanin dillancin labaran Associated Press yace jami’an tsaro sunyi musayar wuta da masu zanga zanga a harabar ma’aikatar harkokin cikin gida a tsakiyar birnin Tunis.Wakilan kamfanin AP sun bada labarin ganin mutane biyu kwance a kasa,sai dai basu da masanaiyar ko sun mutu.
Jiya Asabar ce aka rantsar da kakakin majailisar dokokin kasar Fouad Mebazza,kwana daya bayan da shugaban kasar Zine El-Abdine Ali, ya tsere zuwa Saudiyya.
Sabon shugaban rikon yace ya umurci PM kasar ya kafa gwamnatin hada kan kasa.
Majalisar tsarin mulkin kasar tace sabon shugaban yana da wa’adin kwana 60 na kaddamar da sabon zabe.