A duk lokacin da aka duba sararrin samaniyar yankin gabashin Amurka, za’a ji wani irin shuru, babu motsi idan ba na iska ba. Hakan kuwa nada nasaba da yadda ake cigaba da kara samun karancin wasu nau’ukan tsuntsaye a duniya.
Yawan tsuntsaye na kara raguwa, wanda wani bincike ya tabbatar da cewar ya zuwa yau an samu raguwar yawaitar tsuntsaye fiye da billiyan 3 daga shekarar 1970, a kasashen Amurka, Canada, da Mexico da kashi 29% cikin 100%.
Masu binciken halitar tsuntsaye sun kira wannan karanci na tsuntsaye a matsayin “Annoba mai da komai baya.” Abin takaici shine, wannan yana faruwa akan idon mu, amma bama daukar matakan da suka kamata, sai lokaci ya kure mu koma muna cizon yatsa, inji marubucin wannan rahoton Kenneth Rosenberg na jami’ar Cornell dake nan Amurka.
Fiye da kashi 90% cikin 100% na nau’ukan da su kafi bacewa sun hada da wasu jinsin tsuntsaye 12, har da wadanda jama’a suka shaku da su. An kuma ta’allaka wannan koma bayan da irin yadda mutane ke noma da kuma karuwar dumamar yanayi.
Facebook Forum