Tsohuwar shugabar Liberia Elleh Johson Sirleaf, ta lashe kyautar lambar yabo ta Mo Ibrahim,lamabar da takeyabawa shugabanni da suka nuna kwarewa da kyautatawa a shugabancin su a Africa, kayautar ta hada da kudi dalar Amurka Miliyan Biyar.
Ellen ta kammala wa'adinta a watan da ya gabata, wanda shine chanjin mulkin dimokradiyya na farko a Liberia tun shekara 1944. Uwargida Sirleaf, wacce kuma ta sami lambar yabo ta Nobel, itace mace ta farko da ta taba zama shugabar kasa a Africa, tayi wa'adi biyu, kowanne na tsawon shekaru 6, amman kundin tsarin mulkin kasar bai bata damar ta sake tsayawa takara ba.
Doctor Salim Ahmed Salim, shugaban kwamitin bayar da kyautar ta MoIbrahim ya fada a lokacin da yake bayyana kyautar cewa Ellen ta karbi shugabanci a Liberia a lokacin da yakin basasa ta gama ragargaza kasar, kuma tayi kokarin kawo zaman lafiya da gina kasar da kuma cibiyoyin dimokradiyya. Ya kara da cewa duk da nasarar da aka samu tilas a sami wasu kura-kurai, duk da haka Sirleaf ta aza tubalin da yanzu za a iya ci gaba gina Liberia a kai.
Tsohuwar jakadiyar Amurka a Liberia, Linda Thomas- Greenfield ta ce Ellen ta bar kasar a yanayin da yafi hali data sami Laberiya a ciki, ta kara da cewa akwai sauran jan aiki a gaba.
Facebook Forum