Isabel dos Santos, tsohuwar shugabar kamfanin mai na kasar Angola, Sonangol, ta musanta zargin da magajinta ya yi cewa ta gudanar da wadansu huldar kasuwanci da suka shafi kamfanin da ake da alamar tambaya a kai.
A cikin sanarwa mai tsawon shafi goma sha uku da ta fitar ranar Lahadi, Dos Santos, macen da tafi kowacce mace arziki a Afrika, wadda mujallar harkokin kasuwanci ta Forbes ta yi kiyasin cewa, kudin da take dashi ya kai dala miliyan dubu biyu da dari shida, ta musanta abinda ta kira bata suna da ake yi mata.
Makon da ya gabata, shugaban kamfanin Sonangol, Carlos Saturnino ya bayyana cewa, wani binciken da aka gudanar a cikin kamfanin ya nuna wata huldar kasuwanci ta dala miliyan talatin da takwas da wani kamfani dake Dubai wadda Santos ta amince da ita jim kadan a bayan da AKA SAUKAR DA ita daga kan kujerar shugabancin kamfanin a watan Nuwamba, bayan watanni goma sha shida a matsayin.
Dos Santos ta kare huldar kasuwancin da cewa, an biya kudin ne ga kwararru da aka tuntuba kuma bai sabawa ka’ida ba. Tace ta gudanar da aikinta ne kamar yadda doka ta tanada har zuwa lokacin da za a rantsar da wanda zai maye gurbinta.
Ranar Jumma’a mai shigar da kara na kasar Angola ya bayyana cewa, yana nazarin zargin da Saturnino ya yi.
Mahaifin Dos Santos, Jose Eduardo dos Santos, wanda ya shugabanci Angola daga shekarar dubu da dari tara da saba’in da tara zuwa watan Satumba bara, shine ya nada ta shugabar kwamitin darektocin kamfanin mai na Sonangol. Shugaban kasar da ya gaje shi, Joao Lourenco ya sauke ta daga mukamin, wanda ya ci alwashin yaki da cin hanci da rashawa da ya gurguntar da tattalin arzikin kasar.
Facebook Forum