Tsohon shugaban kasar Ivory Coast Laurent Gbagbo ya bar kasarshi zuwa birnin Hague bayanda kotun bin kadin manyan laifuka ta kasa da kasa ta bada takardar sammacin kama shi.
Lauyen Mr. Gbagbo a Abijan, ya tabbatar da cewa tsohon shugaban kasar ya bar kasar ne a wani jirgin sama na musamman da ya tashi zuwa Netherlands kai tsaye.
An ba tsohon shugaban kasar Ivory Coast din takardar sammacen ne jiya Talata. Yana karkashin daurin talala a wani kungurmin kauye dake arewacin kasar bayan da dakarun kasa da kasa suka hambare gwamnatinshi watanni bakwai da suka shige.
Kotun bin kadin laifukan ta kasa da kasa tana bincike kashe-kashe da fyade, da sauran laifuka keta hakin bil’adama da aikata yayin fadan tsawon watanni biyar da aka yi bayan zaben kasar Ivory Coast. Tashin hankalin ya barke ne sakamakon kin mika mulki da Mr. Gbagbo yayi ga abokin hamayyarshi Alassane Quatarra bayan ya fadi zaben shugaban kasar da aka gudanar a watan Nuwamba shekara ta dubu biyu da goma.
Babban mai shigar da kara na kotun bin kadin manyan laifuka ta kasa da kasa ya fara bincike cikin watan Oktoba domin gano rawar da Mr. Gbagbo ya taka wajen aikata laifukan yaki.