Tsohon shugaban kasar Amurka Bill Clinton yayi kira ga kungiyoyi agaji dake tallafawa wajen yakar cutar kanjamau da su yi kyakkyawan kula wajen amfani da tallafin da suke samu daga kasashe masu arziki. Mr. Clinton ya bayyana haka ne yau Litinin a wajen taron koli na kasa da kasa da ake gudanarwa kan cutar kan jamau a Vienna. Tsohon shugaban kasar ya shaidawa kungiyoyin yaki da cutar kanjamau cewa cibiyoyi da dama suna kashe makudan kudade wajen tura ma’aikatan yaki da cutar taruka. Bisa ga cewarshi, dak wata dala da aka barnarta, tana jefa wani rai cikin hadari. Mr Clinton ya kuma kare kokarin gwamnatin shugaba Barack Obama na tallafawa yaki da cutar kanjamau yayinda Mr. Obama ke shan suka cewa, ya saba alkawarin da ya yin a kara yawan kudin da ake kashewa kan yaki da cutar kanjamau.
Tsohon shugaban kasar Amurka Bill Clinton ya yi kira ga kungiyoyin yaki da cutar kanjamau su kula da tallafin da suke samu
Tsohon shugaban kasar Amurka Bill Clinton ya yi kira ga kungiyoyin agaji dake tallafawa wajen yakar cutar kanjamau su yi kyakkyawan amfani da tallafin da suke samu daga kasashe masu karfin arziki.