Tsohon sakataren wajen Birtaniya kuma shugaban kungiyar ceto 'yan gudun hijira ta kasa da kasa wato International Rescue Committee (IRC) David Miliband ya kawo ziyara Najeriya ya kuma ziyarci jihohin Borno da Adamawa.
A ziyarar David Miliband ya gana da 'yan gudun hijira. Ya ga halin da mata da kananan yara ke ciki kuma ya nuna damuwarsa game da yadda rikicin Boko Haram ya tagayyara fararen hula.
Yace manyan kasashen duniya sun mance da halin da 'yan gudun hijiran Najeriya ke ciki. Yace amma kungiyarsa tana kokari domin taimaka masu ta fuskan kiwon lafiya da bada ilimi da farfado da tattalin arziki. Halin da ake ciki a arewa maso gabas tamkar wani bala'i ne na boye. Yace zai yi anfani da abun da ya gani a ziyarar domin neman goyon baya da kuma neman taimako saboda halin da ake ciki yanzu.
Alkalumma sun nuna kimanin mutane miliyan uku ne rikicin Boko Haram ya raba da gidajensu. Bayan 'yan gudun hijiran dake cikin Najeriya haka akwai wadanda suka jetara zuwa kasashe kaman Kamaru da Nijar da Chadi. To saidai cikin 'yan kwanakin nan hukumomin Kamaru na tasa keyar 'yan Najeriya zuwa gida a wani yanayi na wulakanci.
Wadanda aka turosu zuwa Najeriya sun bayyana irin wahalun da suka sha. Wasu haka aka koresu ba tare da daukan komi ba banda rigunan da suke jikinsu.
Hukumar bada agajin gaggawa NEMA tare da wasu kungiyoyi su ne suke kula dasu. Alhaji Sa'adu Bello shugaban NEMA a jihar Adamawa yace sun yi masu kyakyawan tanadi dangane da abun da zasu ci da wuraren kwana da kula da lafiyarsu.
Ga karin bayani.