Wani mazaunin garin Ile-Ife Alhaji Sani Sarkin Yakin Ile-Ife shi ya shaidawa Muryar Amurka irin taimakon da Alhaji Attahiru Bafarawa da Kiristoci mazauna Sabon Garin suka ba hausawan da rikici ya rutsa dasu.
Alhaji Sani ya tabbatar cewa Bafarawa ya kawo masu taimakon kudi na Naira miliyan goma. Haka ma kiristoci mazauna Sabon Garin na Ile-Ife suka kai Naira dubu dari biyu tare da yin tur da kisan gilla da Yarbawan Ile-Ife suka yiwa Hausawa mazauna garin.
Inji Alhaji Sani zasu yi anfani da taimakon wurin kula da mutanen da basu da lafiya da sauran abubuwan da suka cancanta. Baicin hakan ya kira gwamnatin tarayyar Najeriya ta taimaka ta gyara masu gidajensu da aka kona.
Yace tunda Ile-Ife tana cikin Najeriya zasu cigaba da zama a garin saboda 'yan asalin Ile-Ife din suna zaune wasu sassan kasar kuma babu wanda ya takura masu ko yaci mutuncinsu.
Ga rahoton Hassan Umar Tambuwal da karin bayani.
Facebook Forum