A Burkina Faso, jami'an zaben kasar sun ce tsohon Firayim Ministan kasar a zamanin mulkin Blaise Compaore kamin su raba gari, Marc Chrisitina Kabore shine ya lashe zaben shugaban kasa, wanda ya bashi damar zama shugaban kasar dake Afirka ta Yamma a karon farko cikin shekaru masu yawan gaske.
A gabanni a bayyana sakamakon zaben wanda ya nuna Kabore ya sami kashi 53 cikin dari, kuma kwariya-kwariyar zaben ya nuna abokin takararsa wanda yake biye da shi Zephirin Diabre, ya sami kashi 30 cikin dari na kuri'u da aka kada. Kamfanin dillancin labarai na Faransa a cikin rahoto da ya turo daga Ouagadougou, yace Diabre yayi tattaki zuwa helkwatar Kabore inda ya taya shi murna.
Mutane milyan biyar ne suka yi rajista domin zaben daya daga cikin 'yan takara 14 da suke neman su shugabancin kasar. Da farko an ayyana zaben cikin watan Oktoban bana, amma aka jinkirta shi na wani dan lokaci saboda juyin mulkin da bai sami nasara ba.
Tun bayan samun 'yancin kan kasar a 1960 mahukuntan kasar sun kai ga shugabancin ne ta wajen amfani da karfi, wato yin anfani da karfin soji.