Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsohon Dan Wasan Ghana Raphael Dwamena Ya Rasu A Albania


Dwamena a tsakiya sanye da farar jesi a wata karawa da Amurka a 2017
Dwamena a tsakiya sanye da farar jesi a wata karawa da Amurka a 2017

Hotunan bidiyo da suka karade kafafen sada zumunta, sun nuna yadda dan wasan ya yanke jiki ya fadi shi kadai a filin ana tsakiyar wasa a minti na 24.

Tsohon dan wasan gaba na kasar Ghana Raphael Dwamena ya rasu bayan da ya yanke jiki ya fadi a wani wasan gasar kwallon kafar kasar Albania.

Hukumar kwallaon kafar kasar ta Albania ce ta tabbatar da mutuwar Dwamena mai shekaru 28 da haihuwa.

Hotunan bidiyo da suka karade kafafen sada zumunta, sun nuna yadda dan wasan ya yanke jiki ya fadi shi kadai a filin ana tsakiyar wasa a minti na 24.

Hakan ya sa sauran ‘yan wasan suka ruga kansa don duba halin da yake ciki, amma duk da daukin gaggawa da jami’an lafiya suka kai masa, sai da rai ya yi halinsa.

Nan take aka dakatar da wasan lokacin ana daya da daya.

Dwamena shi ne dan wasan da ya fi yawan kwallaye a gasar Albania Super League da kwallaye tara.

Sau takwas yana bugawa Ghana wasa inda ya ci kwallaye biyu.

Dwamena ya taba bugawa kungiyoyin Levante da Zaragoza a gasar La Liga ta Sifaniya.

Dandalin Mu Tattauna

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG