Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

TSAKA MAI WUYA: Martanin Jam’iyyun NNPP Da APC Kan Hukuncin Da Kotun Zabe Ta Yanke A Kano, Kashi Na Biyu – Oktoba 03, 2023


Aliyu Mustapha Sokoto
Aliyu Mustapha Sokoto

Shirin 'Tsaka Mai Wuya' na wannan makon, zai kawo muku kashi na biyu na muhawara mai zafi da aka fafata tsakanin Shugaban jam'iyyar NNPP ta jihar Kano Hashimu Sulaiman Dugurawa da Jigo a jam'iyyar APC ta jihar Kano Mukhtar Ishaq Yakasai kan hukuncin da kotun sauraran korafe-korafen zaben gwamna a jihar Kano da ke Najeriya ta yanke na zaben gwamna da aka yi na ranar 18 ga watan Maris, 2023.

Kotun dai ta soke zaben Gwamna Abba Kabir Yusuf (Abba Gida-Gida) na jam’iyyar NNPP, inda ta ayyana sunan Nasiru Yusuf Gawuna na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben.

Saurari shirin cikin sauti:

TSAKA MAI WUYA: Martanin Jam’iyyun NNPP Da APC Kan Hukuncin Da Kotun Zabe Ta Yanke A Kano 12'29 .mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:29 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG