Wani dillalin dabbobi mai suna Hassan Sokoto ya ce "gaskiya cinikin bana da na bara ba za’a kwatanta ba, domin kuwa a bara an fi samun ciniki sosai fiye da bana" abin da kuma suka alakantawa da rashin tsaro a yankunan da ake samun dabbobin a Arewacin Najeriya, sabili da hare-haren yan bindiga.
Ya ce ta fuskanr masu saye kuma babu kudi a hannun jama’a duk da cewa masu sayen na son saye.
Farashin ragunan dai inji shi sun kama daga naira dubu 60 har zuwa dubu dari da talatin.
Shi ma wani mai sayen raguna a kasuwar cewa yayi matsalar coronavirus ta karawa dabbobi tsada.
Sarkin kasuwar Alabar Rago umaru dagogo sokoto yace matsalar tsaro ya yi matukar taimakwa wajen tsadar raguna a bana, musanman daga arewa zuwa kudancin najeriya, inda ake da kasuwannin dabbobi na kasa da kasa.
Yanzu dai a yayinda ake ta hidimar saye da sayar wan a dabbobi da sauran kayan masarufi, fatan yan najeriya shine na samun abin cefane da domin samun nasarar gudanr da bikin sallah cikin wadata da kwaucin hankali.
Saurari karin bayani daga Babangida Jibril a sauti:
Facebook Forum