Tottenham ta fidda wani bayani dake cewar ta samu ribar zunzurutun kudi da ya kai fam miliyan £113, bayan ta cire kudaden haraji a kakar wasannin shekarar da ta wuce.
Tottenham ta dara abokiyar hamayyarta Liverpool, wacce take matsayi na biyu a samun riba, inda a shekara ta 2017 zuwa 2018, ta samu fam miliyan
£106.
Kudin da Tottenham ta samu, ya hada da yadda magoya bayanta ke shiga filin wasan Wembley, domin kallon wasannin da ta ke yi, bayan haka, da irin rawar da ta taka a gasar cin kofin Zakarun turai, Uefa Champions League.
Kididdigar ta fito ne bayan da Tottenham ta bude sabon filin wasan ta, da ya ci ma kudi har fam biliyan daya, na kasar Ingila, duk da ya ke ta hada da amsar wasu kudade a matsayin bashi.
Tottenham ta kara samun kudin shiga daga bangaren wasanni Firimiya liga daga fam miliyan sha tara zuwa fam miliyan £42.6..
A wasan da Tottenham ta buga na farko a sabon filin wasanta ta samu nasarar doke Crystal Palace da ci 2-0 ranar Laraba cikin wasan kwantai na Firimiya liga bana.
Inda a yanzu ta ke matsayi na uku a kan teburin firimiya mako na 33, da maki 64.
WASHINGTON D.C. —
Facebook Forum