WASHINGTON, DC —
Rahotanni sun nuna cewa Filani da Tivabe na kashe juna a jihar Taraba. lamarin da ya sa shugabannin kabilun suka kira a yi sulhu.
Rikicin Tivabe da Filani dake faruwa a wasu sassan jihohin Benue da Taraba na daukan wani sabon salo. Rikicin ya soma rutsawa da kabilun dake iyakar jihohin biyu wadanda ma ba Tivabe ba ne ko Filani. Adadin wadanda aka kashe na karuwa tare da wadanda aka rabasu da gidajensu a kauyukan da wasu garuruwan dake kan iyakokin jihohin.
Wani Abdulhadi Ahmad wanda ba Bafillace ba ne yace a garuruwansu biyu duk an koresu babu wani Musulmi daya da ya rage. Ban da haka akwai wasu mutane bakwai da ba'a san inda suke ba. Wasu ganao kuma sun tabbatar da an kashe mutane uku a wani kauye. Kawo yanzu dai an kashe mutane 13.
Yayin da rikicin ke cigaba wasu shugabannin Tivabe da Filani sun bukaci a nemi teburin sulhu. John Zunguwa wani tsohon kwamishana a jihar Taraba kuma shi ne shugaba Tivabe a jihar yace lokaci yayi da kabilun biyu zasu sasanta. Yace idan an koro Filanin dake Benue su kuma Tivaben Taraba me suka yiwa Filani da zasu kama kashesu. Yace a wasu yankunan jihar inda Tivabe suke Filani sun kone kauyukansu. Babu Tivi daya da yake cikin gidansa yanzu. Domin haka yace shi da shugabannin Filani su nemi yin sulhu domin cigaban jihar. Yace a kirashi tare da shugaban Miyetti Allah.
Shi ma shugaban Miyetti Allah na jihar Alhaji Umar Danburam ya kira a sasanta. Yace a yi kiran gaggawa a kawo shugabannin bangarorin biyu a zauna a tattauna.