Rahotanni daga Najeriya na cewa dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar APC mai mulki Bola Ahmed Tinubu, ya zabi tsohon gwamnan jihar Borno Sanata Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa a zaben 2023.
Tinubu ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da ya yi da manema labarai a Daura, a lokacin da ya kai wa shugaban kasa Muhammadu Buhari ziyarar gaisuwar Sallah.
A cewar Tinubu, Shettima mutum ne da ya “cancanta, wanda kuma za a iya dogaro da shi a matsayin abokin takara.”
A ko da yaushe, akan ga Shettima cikin tawagar Tinubu yayin da yake karade sassan Najeriya don nuna godiya ga ‘ya’yan jam’iyyar bayan da ya lashe zaben fitar da gwani a matsayin dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar APC.
Tun gabanin hakan ma, ya kasance mutum na gaba-gaba da ya jajirce don ganin an zabi Tinubu a zaben fitar da gwani.
“Tinubu ya taka muhimmiyar rawa wajen samun nasarar Buhari, ina mai tabbatar maka da haka, saboda ni ina daya daga cikin mutanen da suka kafa jam’iyyar APC.” Shettima ya fada a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels.
Tsananin goyon bayan da Shettima ya nunawa Tinubu, ya sa a lokacin hirar ya bayyana cewa mataimakin shugaban kasa mai ci Farfesa Yemi Osinbajo, ba zai iya shugabancin Najeriya ba.
“Osinbajo mutum ne na kwarai, yana da kirki, amma matsalar ita ce, mutane masu kirki ba sa iya zama shugabannin kwarai. Kamata ya yi ya koma sayar da kankarar ice cream.” Shettima ya fada yayin hirar, ko da yake ya fito ya ba da hakuri kan wadannan kalaman nasa.
Bayyana Shettima a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar ta APC na zuwa ne jim kadan bayan da Alhaji Ibrahim Masari da Tinubu ya zaba da farko, ya janye takararsa a ranar Lahadi.
"Bayan tuntuba da shawara da na nema daga wurare da dama, ina mai sanar da janye takarata.
“Duk da cewa na sauka, na yi imanin cewa, ina da rawar da zan iya takawa don ciyar da jam’iyyarmu da kasarmu gaba a matakai da dama.” Masari ya ce cikin wata wasika da ya aikawa jam'iyyar.
Makonnin da suka gabata, Tinubu ya dauki Masari a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa a mataki na wucin gadi, a kokarin jam’iyyar na cin ma wa’adin da hukumar zabe ta INEC ta gindaya na rufe karbar ‘yan takara.
Gabanin zabin Shettima, an yi ta muhawara da ce-ce-ku-ce kan batun fitar da ‘yan takarar shugaban kasa da mataimaki daga wani bangaren addini daya.
An haifi Shettima a ranar 2 ga watan Satumbar 1966, sunan matarsa Nana Shettima, suna kuma da yara uku, mata biyu na miji daya.
Ya yi wa’adi biyu a matsayin gwamnan jihar Borno, kuma shi ke wakiltar Borno ta tsakiya a majalisar Dattawa Najeriya a yanzu.
Ya yi karatunsa a fannin ilimin tattalin arzikin noma a digirinsa na farko a Jami’ar Maiduguri, kana ya yi diriginsa na biyu a wannan fanni a Jami’ar Ibadan da ke jihar Oyo.
Gabanin ya tsunduma harkar siyasa, Shettima ya taba yin aikin banki.