Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya umarci rundunar 'yan sandan kasar ta samar da tsaro a sakatariyoyin kananan hukumomin jihar Ribas daga kutsen masu cinna wuta da mabarnata.
Mai magana da yawun shugaban kasar, Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan a sanarwar da ya fitar a yau Litinin bayan da batagarin dake adawa da sakamakon zaben kananan hukumomin da ya gudana a Asabar da ta gabata suka banka wa wasu daga cikin sakatariyoyin kananan hukumomin jihar wuta.
"Shugaba Tinubu ya umarci 'yan sanda su dawo tare da tabbatar da zaman doka da oda nan take."
A yayin da yake umartar hukumomin tsaro su shawo kan halin da ake ciki, ya kuma jaddada bukatar ba da kariya da tsaro ga cibiyoyin gwamnati.
"Shugaba Tinubu ya kara da cewa wajibi ne a kare gine-ginen gwamnati da aka gina da kudin al'umma daga barayi da mabarnata"
An samu barkewar rikici a akalla kananan hukumomi 4-tare da cinna wa wani bangare na gine-ginen majalisun kananan hukumomin Eleme da Ikwere da Emohua wuta, sannan an yi harbe-harben kan mai uwa da wabi a Ahoada ta Gabas domin nuna turjiya ga sabbin jami'an karamar hukumar.
Cinna wa sakatariyoyin kananan hukumomin wuta ya biyo bayan janye jami'an 'yan sandan dake bada tsaro ga ilahirin kananan hukumomin jihar 23 da kwamishinan 'yan sandan jihar ya yi.
Dandalin Mu Tattauna