Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, ya rantsar da sabbin ministoci bakwai da ya nada a karshen watan da ya gabata.
Bikin rantsar da Ministoci ya gudana ne a babban dakin taro na Majalisar Gudanarwa da ke Fadar Aso Rock a Abuja.
Ministocin sun hada da Ministar Ilimi, Suwaiba Said Ahmad, Ministar Masana’antu da cinkayya da saka hannun jari, Jumoke Oduwole, Ministan Ayyukan Jin-kai da rage radadin talauci, Nentawe Yilwatda,Ministan Kwadago, Muhammadu Maigari Dingyadi da Bianca Ojukwu a matsayin karamar Ministar harkokin waje.
Sauran sun hada da Ministan gidaje da raya alkarya, Yusuf Abdullahi, karamin Ministan kiwon dabbobi Idi Muktar Maiha.
Rantsar da Ministocin na zuwa ne kwanaki bayan da Majalisar Dokoki ta kammala tantance su.
A ranar 23 ga watan Oktoba Tinubu ya yi wa majalisar zartarwar tasa garanbawul inda ya sauke wasu ministoci ya kuma hade wasu ma’aikatu.
Dandalin Mu Tattauna