Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tinubu Ya Gaji Bashin Naira Tiriliyan 87.38 - DMO


Shugaba Bola Tinubu (Hoto: X/Bayo Onanuga)
Shugaba Bola Tinubu (Hoto: X/Bayo Onanuga)

DMO ya bayyana hakan ne a kokarinsa na fayyace gaskiyar wani rahoto da ke cewa gwamnatin Shugaba Tinubu ta gaji bashin Naira tiriliyan 21 wanda ya karu zuwa Naira tiriliyan 142.

Ofishin kula da basussuka na Najeriya (DMO) ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya gaji jumlar bashin Naira tiriliyan 87.38 lokacin da ya karbi mulki.

Shugaba Tinubu ya hau kan karagar mulki ne a ranar 29 ga watan Mayun 2023.

DMO ya bayyana hakan ne a kokarinsa na fayyace gaskiyar wani rahoto da ke cewa gwamnatin Shugaba Tinubu ta gaji bashin Naira tiriliyan 21 wanda ya karu zuwa Naira tiriliyan 142.

A sanarwar da DMo ya fitar a jiya Litinin, ofishin ya ce ainihin jumlar yawan bashin da ake bin gwamnatin Najeriya izuwa ranar 30 ga watan Yunin 2023, bayan da Shugaba Tinubu ya karbi rantsuwar kama aiki ya kai Naira tiriliyan 87.38.

A cewar ofishin, adadin ya hada da basussukan da ake bin gwamnatin tarayyar Najeriya a ciki da wajen kasar, da jihohi 36 da kuma babban birnin tarayya (Abuja).

“Jumlar yawan bashin da ake bin gwamnatin Najeriya zuwa ranar 30 ga watan Yunin 2023, wanda sune alkaluman farko na bashi bayan hawan Shugaba Bola Ahmad Tinubu kan karagar mulki (a ranar 29 ga watan Mayun 2023), shi ne Naira tiriliyan 87.38, amma ba Naira tiriliyan 21 ba kamar yadda ake yadawa a kafafen yada labarai.”

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG