Wata jami’ar asibiti dake Damagaram ta fadakar da mata game da riga kafin sankarar mahaifa, da cutar Sida da kuma bada tazara tsakanin haihuwa.
Dr, Jakite, mai duba mata a babbar asibitin Damagaram, tace ganin yadda matsalar take Kamari shine dalilin fadakar da matan, akan tazarar haihuwa domin a cewar ta hakkan nada mahimmanci domin yana rage mace macen yara kanana da iyaye mata.
Ta kara da cewa gwamnati ta kara masu karfin gwiwa da samarda magunguna domin a taimakawa mata da maza da kuma yara kanana domin su kasance masu koshin lafiya. Ta kuma ce akwai bincike na sankarar mahaifa da na HIV ko SIDA wanda take karfafawa mata gwiwar su tabbatar da cewa sunyi wannan bincike wanda za’ayi masu shi cikin zuri .
Suma matan da suka halarci taron sun nuna kamsuwarsu ga tasiri fadakarwar ga lafiyarsu dana ‘ya’yansu, wasu kuma sun bada shawarar cewa zuwa asibiti karbar maganin tazarar haihuwa baya likita ya gwada mace shine yafi dacewa ba sayansa a katin magani ba.
Facebook Forum