Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tattalin Arzikin Nijeriya


Hukumar sa ido kan hada-hadar hannayen jarin Nijeriya ta kori shugabarta bayan ta zarge tad a rub da ciki kan kudade da kuma rashin iya shugabanci.

An tsige Shugabar Hukumar kula da hada-hadar hannayen jarin Nijeriya bayan an zarge ta da da laifin al’undahana da kuma rashin iya aiki.

Wani mai magana da yawun hukumar y ace an kori Darakta-Janar Ndi Okereke-Onyuike da yammacin Laraba da kuma babban shugaban hukumar da sauran mambobin hukumar gudanarwar hukumar.

Hukumar t ace an yi hakan ne don a gamsar da jama’a saboda yawan koke-koke game da rashin tafi da al’amura yadda su ka kamata a hukumar, da kuma matsalar shugabanci da kararraki da dama da hukumar ke fuskanta.

Ada dai sai a watan Nuwamba Okereke za ta yi ritaya.

A yanzu dai an nada Mr. Emmanuel Ikazoboh, wanda tsohon babban manaja ne a kamfanin hada-hadar kudi na Deloitte da ke Yammaci da Tsakiyar Afirka, a matsayin sabon shugaban hukumar na wucin gadi

XS
SM
MD
LG