Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tattalin Arzikin Ghana Zai Kai GHC Triliyan 1 (Biliyan $84) Na GDP a Shekarar 2024


Ministan harkokin kudin Ghana, Ken Ofori Attah
Ministan harkokin kudin Ghana, Ken Ofori Attah

Gwamnatin Ghana ta yi hasashen cewa tattalin arzikin kasar zai kai Ghana-Cedi (GHC) Triliyan 1 (kimanin dala biliyan $84) na GDP a shekarar 2024, yayin da ta janye wasu haraji domin rage wa al’umma radadin matsalar tattalin arziki da kasar ke fuskanta.

Ministan harkokin Kudi, Ken Ofori-Atta, ne ya bayyana hakan, a bayanin kasafin kudin 2024 ga majalisar dokoki kamar yadda kundin tsarin mulkin 1992 ya ba shi ikon yi a madadin shugaban kasa.

Ministan harkokin kudi na Ghana, Ken Ofori Attah, da yake bayanin kasafin kudin 2024 ya ce, “Kasafin kudin 2024 ya na da mahimmanci kwarai saboda za mu samu GHC tiriliyan 1 na GDP a karon farko a tarihin tattalin arzikinmu, daga GHC biliyan 219.5 a 2016. Hauhawar farashin kaya ya fara raguwa daga kashi 54.1 a watan Disamba na 2022 zuwa kashi 35.2 a watan Oktoba 2023; tattalin arzikin ya dago da kashi 3.2 cikin 100 a farkon kwata biyu na wannan shekarar."

Haka kuma Ministan ya zayyana yunkurin gwamnati na rage wa ‘yan kasa da kamfanoni radadin matsalar tattalin arziki ta hanyar janye wasu haraji, da suka hada da harajin VAT akan atamfofi na cikin gida na tsawon shekaru biyu, da harajin motocin lantarki don jigilar jama'a na tsawon shekaru 8, da harajin kayayyakin da ake amfani da su a asibitoci, harajin audugan mata da ake yi a cikin gida, an kuma janye harajin shigowa da injuna da motocin noma, da harajin magungunan da ake shigowa da su daga waje.

Malam Nuhu Eliasu, wani Malamin tattalin arziki da harkokin kudi a jami’ar Islamiyya ta Ghana, kuma babban darektan dandalin ba da shawarwari, Advocacy and Policy Alternative Forum, ya ce, akwai wasu matakai na janye haraji da aka sa a wannan kasafin kudin, idan gwamnati ta tabbatar da su, to zai kawo wa talakawan kasar nan saukin rayuwa, kamar harajin da aka janye na shigowa da injuna da motocin noma; da harajin kayayyakin da ake shigowa da su daga kasashen waje domin yin magunguna a cikin gida, da kuma na shigowa da magunguna daga kasashen waje.

Sai dai wasu al’ummar kasa sun bayyana wa Muryar Amurka rashin amincewarsu da kasafin kudin bana, domin sun yi tsammanin za a rage kudin man fetur, domin hakan zai kawo sauki. Haka kuma wasu suka bayyana amincewarsu, musamman wasu harajin da aka janye.

Yanzu majalisar dokoki ta kasa, za ta ci gaba da muhawara kan kasafin kudin.

Saurari rahoton Idris Abdallah:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:33 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG