Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tasirin Mayar Da Kayayyakin Tarihin Benin Da Jamus Ta Yi Ga Najeriya


Kayan tarihi da aka sace a masautar Banin
Kayan tarihi da aka sace a masautar Banin

Gwamnatin Najeriya ta bayyana jin dadi matuka ga aikin maido wa kasar kayayyakin al’adu da tarihinta na masarautar Benin dake jihar Edo 20 da kasar Jamus ta yi bayan da turawan mulkin mallaka suka sace su shekaru 120 da suka gabata.

A cewar gwamnati, kayayyakin tarihin na da mahimmancin ga kudurin mayar da hankali a aikin koyarwa ‘yan kasar tarihi a makarantu.

Gwamnatin Najeriya da ta karbi tawagar kasar Jamus mai mambobi sama da 30 da ta yi jigilar kayayyakin al’adun daga cikin kasarta ta bayyana mahimmancin maido da su cikin Najeriyar ne a lokacin karbansu a hukumance a cikin ginin ma’aikatar harkokin wajenta dake birnin tarayya Abuja.

Kayan tarihi da aka sace a masautar Banin
Kayan tarihi da aka sace a masautar Banin

A yayin taron mayar da kayayyakin tarihin, ministan harkokin wajen Jamus, Annalena Baerbock, ta ce wadannan kayayyakin tarihin na da mahimmancin gaske saboda alama ce ta tuna baya da irin tafiya da aka yi a shekaru da suka gabata inda ta yi godiya ga hadin gwiwa da kasarta da Najeriya suka samu don ganin wannan muhimmiyar rana.

Kayan tarihi da aka sace a masautar Banin
Kayan tarihi da aka sace a masautar Banin

Baerbock ta kara da cewa, gwamnatin kasarta ta tabbatar da maido wa Najeriya wadanan kayayyakin tarihin ne saboda hakan na da mahimmanci ga ci gaban tsarin mulkin dimokuradiyya a duniya.

Jakadan Najeriya a kasar Jamus, Yusuf Maitama Tugga, ya bayyana farin cikinsa a lokacin mayar da kayayyakin al’adun, ya na mai cewa wannan matakin zai taimaka wajen farfado da tsarin koyarwa ‘yan Najeriya al’adunsu a makarantu kasancewar a baya an cire darasin koyar da tarihin kasa a cikin jadawalin karatunta.

Kayan tarihi da aka sace a masautar Banin
Kayan tarihi da aka sace a masautar Banin

A nasa bangare, shugaban hukumar kula da ajiye kayayyakin al’adun gargajiya ta Najeriya, Farfessa Abba Isa Tijjani, ya ce abun alfahari ne kasancewar wannan matakin zai mayar da martabar kasa musamman ga yara wadanda suke tasowa da basu da masaniya a kan tarihin gudunmuwar da iyaye da kakaninsu suka bayar a shekaru da dama da suka gabata.

A cewar hukumomin Najeriya, an kiyasta cewa kasar Ingila ta sace sama da kayayyakin al’adun gargajiyar Najeriya dubu 5 a lokacin da take wa kasar mulkin mallaka kuma a baya-bayan nan gwamnatin kasar Jamus ta sha alwashin maidowa Najeriya kayayyakin al’adunta dubu 1 a shekaru masu zuwa.

Idan Ana iya tunawa, gwamnatin Najeriya ma ta kara himma a aikin tabbatar da dawo da sauran kayayyakin al’adunta dake makale a wasu kasashen waje.

Saurari rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:46 0:00
XS
SM
MD
LG