Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tashin Hankalin Senegal Ya Bazu


Zanga-zangar kin gwamnati a Senegal.
Zanga-zangar kin gwamnati a Senegal.

Munanan tashe-tashen hankula na bazuwa a fadin babban birnin kasar Senegal, a inda masu zanga-zanga ke kwarara bisa tituna don yin zanga-zangar bijirewa canza fasalin dokar zaben da aka yi yinkurin yi.

Munanan tashe-tashen hankula na bazuwa a fadin babban birnin kasar Senegal, a inda masu zanga-zanga ke kwarara bisa tituna don yin zanga-zangar bijirewa canza fasalin dokar zaben da aka yi yinkurin yi.

Wakilin Muryar Amurka a birnin Dakar ya fadi jiya Alhamis cewa daruruwan masu zanga-zanga sun mamaye babban dandalin da ke gaban gini Majalisar Dokokin kasar, suna ta jifan ‘yan sandan kwantar da tarzoma da duwatsu.

‘Yan sandan kwantar da tarzoma sun yi ta mayar da martini, ta wajen harbe-harben barkwanon tsohuwa da ruwan zafi, to amman sun yi ta rabewa ne bayan katangar da ke zagaye da Majalisar Dokokin kasar a yayin wannan arangamar ta sa’a guda.

Haka zalika fadan ya bazu har zuwa ta babbar Majami’ar da ked aura da wurin, a inda ‘yan adawa masu zanga-zangar su ka gwabza da magoya bayan Shugaban Senegal Abdoulaye Wade.

Rahotanni daga Senegal sun kuma nuna cewa an yi zanga-zanga a wajejen Pikine da ke bayan birnin Dakar, da kuma birnin Kaolack da ke yankin tsakiyar kasar.

Da ma Majalisar Dokokin Senegal za ta kada kuri’a ne kan wata bukatar doka da jam’iyya mai mulki ta gabatar, wadda za ta rage yawan kuri’un dad an takara ke bukata kafin ya ci zaben shugaban kasa don a rage yiwuwar zuwa zagaye na biyu. Masu adawa da shirin sun ce zai amfani Mr. Wade ne kawai.

Sabuwar dokar da aka so kafawa din za ta tanaji sabon mukamin mataimakin shugaban kasa, wanda masu adawa da shirin ke ganin ana share fage ne wad an Mr. Wade.

XS
SM
MD
LG