Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tashin hankalin Ingila ya hana kwallon Nigeria da Ghana


Tashin hankalin Ingila ya hana kwallon Nigeria da Ghana
Tashin hankalin Ingila ya hana kwallon Nigeria da Ghana

Rigimar da ta kaure a sassa daban-daban na Ingila ta tilasta sa a soke muhimman wassanin kwallon kafa ciki harda na Nigeria da Ghana.

Tashin hankalin dake gudana a kasar Ingila ya janyo soke wasu muhimman wassanin kwallon kafa da aka shirya tsakanin kasashe daban-daban. Bayan mutuwar wani mutum da aka harbe yayinda yake zaune a cikin motarsa a London ne, aka bada sanarwar soke kwallon kafar da aka shirya yi tsakanin Ingila da Netherlands. Haka ita ma kwallon sada-zumunci da aka so yi tsakanin Nigeria da Ghana a nan Ingila din, an soke ta. Aliyu Mustaphan Sokoto ya zanta da shugaban hukumar kwallon kafar Nigeria Alhaji Aminu Maigari wanda yake a can Ingila gameda wannan kwallon:

XS
SM
MD
LG