Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

TARON VOA: 'Yan Matan Chibok Bamu Manta da Ku Ba'


'Ya Majalisar Wakilai Karen Bass a taron tunawa da 'yan matan Chibok
'Ya Majalisar Wakilai Karen Bass a taron tunawa da 'yan matan Chibok

Jiya 'yan matan Chibok su 219 suka cika shekara daya cur a hannun 'yan Boko Haram.

Yau shekara daya cur ke nan da ‘yan kungiyar Boko Haram suka farma makarantar ‘yan mata dake garin Chibok cikin jihar Borno suka kwashe ‘yan mata fiye da 200 suka yi gaba da su.

Wannan lamarin ya harzuka al’ummar duniya inda kasashe daban daban suka yi tur da lamarin tare da yin zanga-zanga.

Duk da cikarsu shekara daya a hannun ‘yan ta’addan, duniya ba ta manta da su ba saboda dalilinsu ya sa Muryar Amurka ta shirya taro na musamman.

Jiya Talata Muryar Amurka ko VOA ta shirya wani taro na musamman a hedkwarta dake Washington DC inda aka yi juyayi akan ‘yan matan 219, har yanzu suna hannun 'yan ta'addan Boko Haram.

Yayin da take jan akalar taron Jamila Fagge, ma’aikaciyarSashen Hausa na Muryar Amurka, ta ce “na yi murna matuka mun kasance a wannan ranar domin mu nuna damuwarmu.”

Cikin wadanda suka halarci taron har da wata Patience Bulus wadda tana cikin ‘yan matan da aka sace amma ta tsallake rijiya da baya tare da wasu.

Yanzu su goma sha daya suna nan Amurka suna cigaba da karatunsu.

‘Yar Majalisar wakilan Amurka ta jam’iyyar Democrat daga jihar California, Karen Bass, da ta halarci taron inda ta ce lamarin ya tayar da hankalin duniya.

Wadanda suka gabatar da jawabai a wurin taron sun hada da Frederica Wilson ‘yar Democrat daga jihar Florida da Emmanuel Ogebe da kungiyarsa ta taimakawa ‘yan matan da suka samu kubuta zuwa nan Amurka inda suke cigaba da karatunsu.

A nan Amurka da lamarin ya faru an mayar da martani nan da nan-inji 'Yar Majalisa Karen Bass.

Ta ce Amurka ta dukufa ta ga an kwato ‘yan matan har ma ta aika da sojoji su taimaka wurin aikin leken asiri da tara bayanai akan inda ‘yan matan suke.

Ita ma ‘yar majalisa Frederica Wilson ta gabatar da wani kuduri a majalisar wakilan Amurka wanda ya yi tur da sace ‘yan matan.

Ba ta tsaya nan ba sai da ta kai ziyarar gani da ido da ji da kunnuwa abin da ya faru zuwa Najeriya.

Ta samu ta gana da ‘yan matan da suka kubuta har da Patience Bulus da yanzu take Amurka.

Ta gana da iyayen ‘yan matan da dama. Ta ce bakin cikin da iyayen yaran ke ciki ya tsoratata.

Har yanzu ‘yan Boko Haram suna rike da ‘yan mata 219. Babu duriyarsu idan ba makon jiya ba da wata ta ce ta ga wasunsu a Gwoza.

XS
SM
MD
LG