WASHINGTON, DC —
Gwamnonin jihohin arewa-maso-gabashin Nigeria sun rattaba hannayensu akan daftarin wani sabin shirin farfadowa da karfin tattalin arzikin jihohin nasu. Haka kuma gwamnonin sun tattauna kan matsalar tsaro wacce ke addabar yankin, musamnman daga hare-haren da kungiyar Boko Haram ke kaiwa akan al’ummominsu. Sai dai a zaman da suka yi a Gombe, an lura da cewa akwai cikas din dake bukatar a kawar da shi kafin a cimma nasarori a fuskar tattalin arziki da kuma tsaro. Daga Gombe, ga rahoton wakilin VOA, Abdulwahab Mohammed:
Tabarbarewar tattalin arzikin jihohin arewa-maso-gabashin Nigeria ya tilastawa gwamnonin jihohin neman mafita.