Dan wasa Tammy Abraham ya ce kungiyar shi za ta iya dogaro da shi don kaiwa ga mataki na gaba wajen shigar da Chelsea gasar Zakarun Turai.
Kwallaye 15 da ya zura sun sa ya ci gaba da kasancewa dan wasan gaba na kungiyar, tun bayan halin damuwa da dan wasa Frank Lampard ya shiga a watan Janairun da ya gabata.
Tun a watan Disamba aka janye takunkumin da aka kakabawa Chelsea na sayen ‘yan wasa, amma dai kungiyar ba ta yi cinikin kowa ba a watan da ya gabata, duk yadda ake alakanta ta da dan wasa Edison Cavani, da Timo Werner.
Dan wasa Olivier Giroud ya kasa tabuka komai a wasan da suka tashi da ci 2-2 a Leicester ranar Asabar, tsakanin Chelsea da Michy Batshuayi.
Abraham ya ce "a gare ni na kasance a wurin da ya dace, a lokacin da ya dace, da yin imani da kaina da kuma iyawa ta. Ina da tabbacin zan sake cin wasu kwallaye kadan." A gare ni ba zan iya yin korafi ba, ta kasance babbar kaka zuwa yanzu.
Ya kara da ceware har yanzu akwai manyan wasannin dake tafe, dole ne in kasance cikin shiri a gare su. Abraham ya yarda cewa zai yi marhabin da gasar a Stamford Bridge bayan kammala wasanninsa na farko na bana.
Facebook Forum