Shugaban Hukumar Samar Da Agajin Gaggawa Ta Jihar Borno, Alhaji Grema Tarab ya jinjina ma Hukumar Raya Kasashe Masu Tasowa Ta Amurka (USAID) saboda dinbin tallafin da gwamnatin Amurka ke bayarwa ta wajen hukumar don taimaka ma yankin arewa maso gabashin Nijeriya da rikicin Boko Haram ya daidaita. Ya ce an ba jihohin Adamawa, da Borno da Yobe sama da miliyan 10.
Alhaji Tarab ya yi kira ga sauran kasashe da kungiyoyi masu zaman kansu da su yi koyi da Amuraka wajen agaza ma wadanda rikicin Boko Haram ya addaba. Ya ce akwai mutane wajen 120,000 da yan kai a wurare kimanin 13 da kuma Kananan Hukumomi 22 a jihar Borno kawai ma.
Ya ce ba za a samu matsala wajen raba kayan agajin ba. Hasalima kwanan baya wakilan gwamnatin Amurka su ka yi zama da su, inda su ka tabbatar masu cewa za a yi gaskiya da adalci wajen rabon kayan tallafin. Y ace su kansu wakilan na Amurka sun gamsu cewa tsarin da ke kasa zai tabbatar da gaskiya da adalci wajen rabon.